✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai hari gidan kurkuku a Filato

Yanzu haka dai an tsaurara matakan tsaro a ilahirin yankin.

An jiyo karar harbe-harbe a ranar Lahadi a gidan gyaran hali da ke Jos, babban birnin Jihar Filato.

Wakilinmu ya gano cewa an fara jin harbe-harben ne wajen misalin karfe 5:30 na yamma.

Yanzu haka dai an tsaurara matakan tsaro a ilahirin yankin da gidan gyaran halin yake.

Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS), Jeff Longdiem, ya yi alkawarin cewa zai kira shi daga baya.