✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

An kai hari gidan Shugabar Majalisar Amurka

An kwantar da mijin Nancy Pelosi a asibiti bayan an kai hari a gidansu

Shugaban Majalisar Dokokin Amurka, Nancy Pelosi, ta auna arziki, bayan wani mahari ya kutsa cikin gidan da tsakar dare yana neman ta.

’Yan sanda sun ce da kyar mijin Shugabar Majalisar, Mista Paul Pelosi, ya sha a harin na karfe 2.30 na dare, kuma yana bukatar kulawar asibiti, sakamakon buga masa guduma da maharin ya yi.

Babban jami’in ’yan sanda na yankin Fransisco, Bill Scott, ya ce, “A lokacin da ’yan sanda suka kai dauki gidan, sun samu wani mutum da mijin Misis Pelosi, Paul, suna kokawa da guduma.

“Wanda ake zargin ya kwace gudumar, sannan ya buga wa Mista Paul Pelosi ita.”

Ya ce za gurfanar da maharin mai shekara 42 a kan zargin cin amanar kasa, yunkurin aikata kisa, kai hari da makami mai kisa, shiga gida ba da izini ba, da sauransu.

Kafofin yada labaran Amurka sun ce fasa gidan da maharin ya yi ke da wuya, ya fara yi wa Mista Paul tsawa yana tambayar sa, “Ina Nancy take,” wanda ya sa ake zargin harin na da alaka da siyasa.

Nancy Pelosi, wadda ita ce ta mutum ta biyu bayan Shugaban Kasar Amurka, tana birinin Washington a lokacin da aka kai harin a gidan nasu da ke Carlifornia.

Kakakin Nancy Pelosi, Drew Hammill a cikin wata sanarwa ta ce, mijin nata mai shekara 82 “yana samun cikakkiyar kulawa a asibiti, da fatan zai murmure.”

Rahotanni sun ce mijin nata ya fara samun sauki bayan aikin da aka yi masa sakamakon harin gudumar.

Bill Scott ya ce har yanzu ba a kai ga gano manufar harin ba da aka kai da misalin karfe 2.30 na dare a agogon yankin.