✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai hari 2 a rana guda a Zangon Kataf

Mazauna yankin suna zargin maharan da nufin kawar da su daga doron kasa

Kasa da awa 24 da kai hari a kauyen Kurmin Masara da ke Masarautar Atyap a Karamar Hukumar Zangon Kataf ta Jihar Kaduna, an sake kai hari a daren ranar Litinin.

Wani makwabcin garin da ya bukaci a sakaye sunansa ya shaida wa Aminiya cewa maharan sun zo kauyen Atisa, da ke yankin Kurmin Masara da misalin karfe 9:50 suka fara bude wuta kan mai uwa da wabi.

“Da maharan suka lura cewa sun ci karfin Kurmin Masara inda yawanci mazauna suka arce bayan harin ranar Lahadi da asuba, shi ne suka saki kai hari unguwan Atisa da shi ma yake yankin Kurmin Masara. A yanzu haka da nake magana da kai (10:45) ina jin karar harbe-harbe,” inji shi.

Da yake tabbatar wa Aminiya da kai harin a daren Litinin, Shugaban Matasan Kabilar Masarautar Atyap, Gabriel Joseph, ya mika kukansa ga gwamnatoci da ta tashi da gaske domin a cewarsa, maharan na da wata boyayyiyar manufa na ganin sun kawar da su daga yankin ko daga bayan kasa.

Ya zuwa lokacin kammala hada wannan rahoton babu bayani game da adadin wadanda suka rasa rayukansu ko dukiyar da aka yi asara.

Kazalika Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ba ta ce komai ba, saboda kokarin jin ta bakin kakakinta, ASP Jalige Mohammed, ya ci tura.