✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kai mummunan hari kan jirage ruwan yakin Rasha

Rasha ta zargi Ukraine da kai mummunan hari da jirage sama marasa matuka kan shalkwatar jiragen ruwan yakinta da ke garin Sevastopol da ke bakin…

Rasha ta zargi Ukraine da kai mummunan hari da jirage sama marasa matuka kan shalkwatar jiragen ruwan yakinta da ke garin Sevastopol da ke bakin gabar teku.

A cewar jami’an Rasha, An soma kai harin ne da misalin karfe 4:20 agogon kasar a inda jiragen sama marasa matuka suka soma luguden wuta.

Gwamnan yankin wanda Rasha ta nada, Mikhail Razvozhaev, ya ce, sojojin ruwan Rasha sun mayar da martanin harin, inda suka kakkabo jiragen saman marasa matuka.

A cewarsa, wannan hari shi ne mafi girma da aka kai wa Rasha a yankin tun lokacin da ta shiga yankin na Krimea a watan Fabrairu.

A harin an lalalata akalla jirgin ruwan yakin Rasha guda daya, sannan babu wani gini na farar hula da harin ya shafa.

Garin Sevastopol shi ne gari mafi girma a yankin Krimiya da Rasha ta kwace a hannun Ukraine a shekarar 2014.