✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai shi gidan yari kan satar dunkulen dandanon girki

Kwali 22 na dunkulen dandanon girki sun yi batar dabo a hannunsa.

Kotu ta tisa keyar wani matashi zuwa gidan yari kan satar dunkunlen dandanon girki a Kano.

Alkalin Kotun Shari’ar Musulunci, Dokta Bello Khalid, ya bayar da umarnin ne bayan an gurfanar da matashin kan zargin sace kwali 22 na dunkulen dandanon girki.

Dan Sanda Mai Gabatar da Kara, Insfekta, ya ce ana tuhumar matashin ne da aikata sata da kuma cin amana bayan wani mai suna Jamilu Ibrahim mazaunin unguwar Galandanci ya kai karar shi a ofishin ’yan sanda na Sabon Gari a ranar 10 ga watan Maris.

Insfekta Wada ya shaida wa kotun cewa Jamilu ya ba wa wanda ake zargin kwali 260 na dunkulen dandanon girki ya ajiye a shagonsa.

Amma da Jamilu ya je karbar kayan sai ya iske kwali 22 na dunkulen dandanon —wadanda kudinsu ya kai N216,000 — sun yi batar dabo.

Amma matashin da ake zargi, mai shekara 37, ya musanta laifin da ake tuhumar shi da aikatawa.

Daga nan ne alkalin kotun, Mai Shari’a Dokta Bello Khalid, ya ba da umarnin a tsare shi a gidan yari, sannan ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 8 ga watan Afrilu.