✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama shi yana wa mai neman aiki fyade

Kotu ta sa a tsare mutumin a gidan yari tukuna.

Wata kotun Majistare da ke Ebutte-Metta a Jihar Legas, ta tsare wani mutum saboda yi wa wata mai neman aiki fyade.

Yayin gabatar da zarge-zargen, mai gabatar da kara ya shaida wa kotun cewa matar ta je wajen wanda ake tuhumar ne don neman agaji don ta samu aiki.

Shi kuma ya yika amfani da kafar yana yaudarar ta yana kwanciya da ita, yana cewa aikin da take nema bai fara ba tukuna.

Mai gabatar da karar ya ce bayan dogon jiran gawon shanu ne matar ta fusata ta kai kara ga ’yan sanda suka cafke shi tare da gurfanar da shi kan aikata fyade da kuma yin garkuwa.

Alkalin kotun, F.F. George, ta ba da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake zargin a gidan yari har zuwa lokacin da za a samu shawarar lauyoyi daga Sashin Gabtar da Kara (DPP).