✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai wa Fira Ministan Libya farmaki

An bude wa motar Fira Ministan wuta a yayin da majalisa ke shirin zaben wanda zai maye gurbinsa

Fira Ministan Libya, Abdulhamid al-Dbeibah, ya tsallake rijiya da baya a wani yunkurin hallaka shi da wasu mahara suka yi a ranar Alhamis.

Maharan sun bude wa motarsa wuta a Tripoli, babban birnin kasar, yayin da yake hanyarsa ta komawa gida.

Sai dai maharan sun tsere bayan rashin samun nasarar hallaka al-Dbeibah.

Tuni aka sanarwar jami’an tsaron birnin Tripoli faruwar lamari kuma nan take suka shiga bincike.

A ranar Alhamis ne ’yan majalisa a Gabashin Libya za su kada kuri’ar zaben wanda zai maye gurbin Mista al-Dbeibah, ko da yake, ya ce ba zai amince da sakamakon kuri’ar ba.

Ya yi gargadin cewar duk wanda aka zaba don maye gurbinsa na iya mayar da kasar baya.

Ana sa ran ’yan majalisar za su iya maye gurbin al-Dbeibah da tsohon Ministan Harkokin Cikin Gidan kasar, Mista Fathi Bashaga.

Ana ta samun tashin hankali tsakanin kungiyoyin da ba sa jituwa da juna a Libya kan wanda ya dace ya jagoranci kasar.