✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kai wa gadar dakon man Rasha harin bom

Bom din ya tashi da wata babbar mota makare da man fetur kuma ya lalata hannu biyu a katafariyar gadar

Wani jirgin kasan dakon mai ya kama wuta a kan Gadar Kerch na kasar Rasha a hanyarsa ta zuwa yankin Crimea na Ukraine da ke karkashin Rasha.

Kwamitin Yaki da Ta’addanci na kasar Rasha ya ce harin bom din mota ne aka kai wa gadar da ke dauke da titin mota da na jirgin kasa.

“Da misalin karfe 6 na safe (3 a asuba GMT) bom ya shafi tarago bakwai na jirgin dakon mai da ke hanyarsa ta zuwa Crimea,” a cewar kwamitin.

Ya ce bom din ya tashi da wata babbar mota makare da man fetur kuma ya lalata hannu biyu a katafariyar gadar mai matukar muhimmanci ga Rasha.

Harin ya yi sanadiyyar dakatar da zirga-zirga ta Gadar Kerch, tare da barazanar tsayar ga jigilar makamai ga dakarun Rasha da ke yaki a Ukraine.

Hukumomin Rasha dai sun ce harin bai lalata bangaren jigilar kaya a kan layin dogon ba.

Sun kuma tabbatar da kafa kwamiti domin gudanar da bincike kan lamarin.