An kai wa gidan dan sanda mai yaki da ’yan ta’adda hari a Zariya | Aminiya

An kai wa gidan dan sanda mai yaki da ’yan ta’adda hari a Zariya

‘Yan sanda
‘Yan sanda
    Aliyu Babankarfi, Zariya

Mahara dauke da muggan makamai sun kai hari gidan ASP Aliyu Umar, daya daga cikin jami’an ’yan sanda da ke aikin yaki da ’yan bindiga a Zariya, Jihar Kaduna.

Maharan da suka kai harin tun da misalin karfe 9:00 na dare, an yi ta artabu da su har kusan karfe 12:00 na daren Litinin, kafin daga bisani jami’an tsaro su kawo dauki.

Majiyarmu ta tabbatar da cewa maharan, sun fito ne ta dajin da ke hanyar makarantar ’yan mata ta Kofar Gayan a kafa, dauke da muggan makamai sannan suka kuma yi wa gidan jami’in kawanya inda sukayi ta harbe-harben kan mai uwa da wabi.

Gidan ASP Aliyu dai na dauke da mutane sama da 20, ko da yake maharan ba su samu nasarar shigarsa ba.

Sai dai akwai yakinin sun hallaka wasu mutum biyu wadanda ake tsammanin masu kiwon shanu ne a wajen Kofar Kona da ke Zariya, kamar yadda wata majiyarmu ta tabbatar.

Majiyar tamu ta ce harin shiryayye ne musamman don a halaka jami’in tsaron da ake ganin yana namijin kokari wajen yaki da ’yan bindigar.

Ta kuma ce jami’an tsaro na ’yan sanda da soja da ’yan sa-kai sun taka muhimmiyar rawa wajen dakile harin, inda bayan sun kori maharan, suka samu nasarar kwato shanu masu yawan gaske da maharan suka kwashe na makiyayan da ke zaune a kusa da wajen.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton dai ba a sami tabbacin yawan mutanen da suka rasa rayuwankansu ba da kuma wadanda akayi awon gaba da su ba.