✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda aka kai wa Kwamishinan Tsaron Sakkwato hari

An kai farmakin ne a lokacin taron magance matsalar tsaro.

Kwamishinan Tsaro na Jihar Sakkwato, Kanar Garba Moyi, ya tsallake rijiya da baya, a wani hari da aka kai gidansa.

Kazalika an kai farmaki a gidan Dagacin Isa da ke Karamar Hukumar Isa a jihar ta Sakkwato.

Aminiya ta gano cewa an kai wa shugabannin harin ne a lokacin da masu fada a ji a garin suk tsaka da gudanar da taro kan matsalar tsaro.

Suna cikin taron ne “Wasu bata-gari suka kutsa ciki suka mamaye gidan kwamishinan tsaro sannan suka cinna wa gidan wuta.

“Daga nan sai suka wuce zuwa gidan Sarkin Gobir Isa inda suka farfasa wasu motoci,” inji majiyarmu, wadda ta ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin ’yan sandan jihar Sakkwato, ASP Sanusi Abubakar, ya ce ’yan sanda na bibiyar lamarin.

Ya shaida wa Aminiya a ranar Talata cewa an kama wasu mutum biyar da ake zargi da hannu a hare-haren.