✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kai wa magoya bayan Atiku hari lokacin da suke lika fastarsa a Ribas

Uku daga cikin mutum biyar din da aka kai wa harin yanzu suna asibiti

Akalla mutum uku na can kwance a asibiti bayan wasu ’yan daba sun kai wa magoya bayan dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar hari a jihar Ribas.

Rahotanni sun ce maharan sun harbi Ko’odinetan kamfen din Atiku na Karamar Hukumar Omuma, Nnamdi Nwogu da kuma Udochukwu Nwakpala, da wasu mutum uku.

An dai kai musu harin ne lokacin da suke lika fastocin dan takarar a yankin Eberi na Karamar Hukumar a ranar Lahadi.

Bayanai sun nuna mutanen sun sami raunuka a saran da aka yi musu da adduna a jikinsu, lokacin da matasan kimanin su 30 suka far musu.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Grace Iringe-Koko, har yanzu bai magantu ba a kan batun.