✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai wa masu aikin rajistar zabe hari a Enugu

Mako biyu bayan mahara sun kona Ofishin INEC na Karamar Hukumar Igboeze ta Arewa a Jihar Enugu

Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan kungiyar IPOB ne sun kai wa jami’an Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ke aikin rajistar katin zabe hari a Jihar Enugu.

An kai wa jami’an hari ne mako biyu bayan mahara sun kona Ofishin INEC na Karamar Hukumar Igboeze ta Arewa a jihar ta Enugu

Kwamishinan INEC na Kasa Kan Sadarwa da Wayar da Kan Jama’a, Festus Okoye, ya ce maharan sun far wa jami’an hukumar ne a lokacin da suke tsaka da aiki, inda suka bude wuta babu kakkautawa, suka tarwatsa kowa.

Ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 2.30 na rana a wata makarantar firamare da ke unguwar Umuopu a mazabar Umuozzi ta 19 da ke Karamar Hukumar Igboeze ta Arewa a Jihar Enugu a ranar Laraba.

“A garin guje-gujen ne aka jikkata wani daga cikin ma’aikatan namu, wanda yanzu haka ana jinyar shi a asibiti.

“Injinan rajistar zabe biyu kuma sun bace tare da kayan jami’an namu, har da wayoyinsu.

“Saboda haka an dakatar da aikin rajistar masu zabe a Karamar Hukumar Igboeze ta Arewa,” in ji Festus Okoye.

Idan ba a manta ba, a ranar 3 ga watan Yuli da muke ciki wasu da ba san ko su wane ne ba sun kona ofishin INEC na karamar hukumar.

Duk da haka, daga baya hukumar ta ci gaba da yi wa masu zabe rajista, kafin harin ranar Laraba, wanda Okoye ya ce bayan aukuwarsa an sanar da ’yan sanda domin su gudanar da bincike a kai.