✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai wa Shugaban Afghanistan harin bom

Shugaban Kasar Afghanistan Ashraf Ghani ya tsallake rijiya da baya daga wani harin bom.

Shugaban Kasar Afghanistan ya tsallake rijiya da baya daga wani harin bom da aka kai masa a safiyar Babbar Sallah.

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Afghanistan ta ce akalla bama-bamai uku ne aka harbo a daidai lokacin Shugaban Kasar zai fara gabatar da jawabinsa na sallah a birnin Kabul da misalin karfe 8 na safiyar Talata.

An ji karar fashewar bama-baman a fadin yankin Green Zone, inda Fadar Shugaban Kasar  da ofisoshin jakadancin kasashe suke.

“A yau makiyan kasar Afghanistan sun kaddamar da hare-haren bom a sassa daban-daban na birnin Kabul, inda rokokin suka lalata wasu wurare uku.

“Muna gudanar da bincike domin tabbatar da girman irin barnar da suka yi,” a cewar mai magana da yawun ma’aikatar, Mirwais Stanikzai.

Mintoci kadan bayan harin, Shugaban Kasar ya fara gabatar da jawabin nasa a gaban manyan jami’an gwamnatinsa.

An sha nufar Fadar Shugaban Kasar Afghaninstan da harin bom, wanda na karshen  aka kai a watan Disamban 2020.

Harin na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar Taliban ta tsananta kai hare-hare a Afghanistan, inda ake sa ran dakarun kasashen waje za su kammala janyewa a karshen watan Agusta.