Daily Trust Aminiya - An kaiwa Sarkin Potiskum hari a hanyar Kaduna zuwa Zariya
Subscribe

An kaiwa Sarkin Potiskum hari a hanyar Kaduna zuwa Zariya

Wasu ‘yan bindiga sun kaiwa Sarkin Potiskum na jihar Yobe Alhaji Umaru Bubaram, hari akan hanyar Kaduna zuwa Zariya.

‘Yan bindigan sun tare titin ne da misalin karfe 9 na dare har zuwa karfe kusan 2 daren jiya Talata.

Rundunar ‘Yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da aukuwar harin da aka kaiwa Sarkin Potiskum akan hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Kakakin rundunar Yakubu Sabo ne ya tabbatar da harin a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.

Ya ce, akalla mutum shida ne suka rasa rayukansu a yayin wannan hari da aka kai.

Yakubu, ya kara da cewa, an kashe mutum hudu daga cikin tawagar Sarkin, sannan an raunata mutum biyar.

A cewarsa an kai wadanda suka ji rauni asibitin Barau Dikko da ke Kaduna.

Ya ce, wasu mutane ne cikin kayan sojoji suka tare titin cikin dare sannan kuma da suka hango tawagar Sarkin Potiskum sai suka bude masa wuta.

Sarkin na ziyartar wasu Sarakuna ne na Arewacin kasar nan domin tattauna shirin kaddamar da babban masallacin Juma’a na Potiskum wanda za’a bude a ranar 18 ga watan nan.

More Stories