✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama AK-47 da harsashi 600 a hannun dillalin makamai a Kaduna

Dubun wani dallalin bindiga ta cika inda ’yan sanda suka kama shi dauke da bindiga kirar AK-47 da harsashi 600. Kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna,…

Dubun wani dallalin bindiga ta cika inda ’yan sanda suka kama shi dauke da bindiga kirar AK-47 da harsashi 600.

Kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige, ya ce an kama dillalin makaman ne a yauyen Madaci da ke yankin Damari a Karamar Hukumar Gwari.

Sanarwa da rundunar ta fitar a Kadunan ta ce mazauna yankin ne suka kai wa ’yan sanda rahoto kan rashin gamsuwa da take-taken mutumin a yankin, wanda bayan rundunar ta zo yankin domin bincike, wanda ake zargin ya yi kokarin arcewa.

Jalige ya ce bincike da rundunar ta yi a motar mutumin kirar Volkswagen ya kai ta ga gano bindiga kirar AK-47.

Bayan an titsiye shi a wurin bincike, mutumin da ake zargin ya bayyana musu wata motar daban da aka gano harsasan a cikinta.

“Mun kuma gano albarusai da aka boye a tankin man motar kirar Volkswagen domin tsallake wa binciken jami’an tsaro” in ji Jalige.