✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama alkama mai guba da ake sayarwa don ci a Gombe

An samar da alkamar ce domin shukawa amma aka karkatar ana sayar wa masu ci

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta kama buhu 80 na alkama mai dauke da magani da ake sayar wa mutane domin ci a Jihar Gombe.

Gwamnatin Tarayya ce ta samar da irin alkamar mai dauke da maganin kwari domin amfanin manoma amma aka karkatar da ita ana sayarwa a kasuwa domin ci.

Shugaban Ofishin Hukumar NAFDAC a Jihar Gombe, Mista James Agada, shi ne ya bayyana hakan a ranar juma’a a ganawarsa da manema labarai a Gombe.

Agada, ya ce sun hukumar ta kama alkamar ce ta hanyar bayanan sirri da ta samu, sannan ta aika jami’inta cikin sirri ya sayo alkamar domin tabbatar da sahihancin rahoton da suka samu.

Yace wanda yake sayarwa mudu-mudu shi ya sanar da su inda babban dillalin alkamar yake har suka iya kama shi suka rufe shagonsa mai dauke da manyan buhuna 80 na alkamar mai magani.

A cewar sa asalin mudun alkamar yakai N600 zuwa N1,000 amma wannnan da ke dauke da maganin da gwamnatin ta samar don manoma aka karkatar, N300 ake sayar da ita.

Ya bayyana cewa alkamar da ke dauke da magani tana da hadari ga lafiya, don haka hukumar take kiran jama’a da su guji sayen ta don ci.

Daga nan sai yace suna ci gaba da gudanar da bincike domin gano ko akwai wasu da suka boye irin wannan alkama don sayarwa jama’a.