✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama babban limamin cocin IPOB da makamai da kayan tsafi a Imo

Rundunar ta ce yanzu ’yan IPOB sun koma buya a coci-coci da wuraren tsafi.

’Yan sanda a Jihar Imo sun ce sun cafke wani babban limamin coci na haramtacciyar kungiyar ’yan awaren Biyafara ta IPOB.

An kuma kwace bindiga guda daya da harsasai biyar da suka hada da wasu abubuwan fashewa da tutar Biyafara da sauran kayayyakin tsubbace-tsubbace.

Wata sanarwa dauke da sa hannun Kakakin rundunar a Jihar, CSP Mike Abattam, ta ce kamen ya biyo bayan samamen da aka kai kan sansanin ’yan kungiyar sannan aka sami nasarar ragargazarsu a Jihar.

Limamin cocin na IPOB da aka kama
Limamin cocin na IPOB da aka kama

Rundunar ta ce bincikenta a yanzu ya nuna cewa ragowar ’yan ta’addan na IPOB sun koma buya a coci-coci da wuraren tsafi.

Sanarwar ta ce, “Mun tabbatar da hakan ne a ranar hudu ga watan Agustan 2021 da misalin karfe 6.20 na yamma, yayin tuhumar wadanda ake zargi da aka kama daga Okporo, a Karamar Hukumar Orlu ta Jihar Imo.

“Daya daga cikinsu ya bayyana cewa yanzu suna fakewa a coci-coci don kai hari kan ofisoshin ’yan sanda, kuma sun jagoranci tawagar ’yan sandan zuwa gidan Ikechukeu Umaefulem, babban limamin kuma jagoran cocin ‘Synagogue Amii’ da ke yankin Akabo a Karamar Hukumar Ikeduru ta Jihar Imo, inda aka kama shi.”

Sanarwar ta kuma ce wanda ake zargin da tsafi yanzu haka yana tsare a hannun rundunar inda ake ci gaba da yi masa tambayoyi, kuma yana taimaka mata da bayanan da za su taimaka a kai ga gano ragowar boyayyun sansanonin kungiyar.