✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama bindigogi 73 da albarusai 891 da aka boye a cikin shinkafa

Wadanda ake zargin sun boye makamai da alburusai a karkashin buhunan shinkafar da ake sarrafawa a cikin gida.

Jami’an Hukumar Hana Fasa-kwauri ta Kasa shiyyar Jihar Kebbi sun kama wasu mutum uku kan fasakwaurin bindigogi gida 73 da kuma alburusai 891.

Wadanda ake zargin sun boye makaman ne a karkashin buhunan shinkafar da ake nomawa a cikin gida.

“An kama mutum uku sannan an tsare su yayin da ake gudanar da bincike,” inji kakakin Hukumar Kwastam ta Kasa, DC Joseph Attah a cikin sanarwar da ya fitar a daren ranar Litinin.

Ya jami’an hukumar bisa ga bayanan sirri  da suka samu game da hanyar Yawuri, gefen ruwan Zamare a Jihar Kebbi, sun tare wata babbar mota makare da shinkafar ‘yar gida tare da wasu buhuna boye a karkashin shinkafar.

Attah ya ce bayan bincike sosai sun gano buhuna dauke da bindigogi 73 da ake kerawa a cikin gida da kuma albarusan 891.

Attah ya yi kira ga mazauna yankin da su ci gaba da ba hukumomin tsaro hadin kai ta hanyar bayar da bayanan sirri da za su taimaka wajen wanzar da tsaro a kasar nan.