✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama boka da kokon kan mutum a Kuros Riba

Ana zarginsa ne da firgita samari da ’yan mata ta hanyar tsibbu.

Jami’an ’yan sanda a Jihar Kuros Riba sun kama wani matashi mai suna Michael Moris Bassey da kokon kan mutum a unguwar Uwanse da ke Karamar Hukumar Kalaba ta Kudu.

Ana zargin Michael ne da firgita samari da ’yan mata a unguwarsu ta hanyar tsibbu.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar, Mista Sikiru Akande ne ya gabatar da wanda ake zargin tare da sauran mutane su 35 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a Kalaba.

Wanda ake zargin ya shada wa Aminiya cewa, “Matsala na samu da wata budurwa, shine ta kira min ’yan sanda, cewa zan kashe ta ta hanyar tsafi, lamarin da ya sa ’yan sanda suka kama ni aka kawo ni nan.”

Sauran wadanda ake zargi sun hada da wasu mata shida da aka kama su a garin Ikom, bisa zargin safarar yara kanana.

Kwamishinan ya ce da zarar an kammala bincike za a mika su ga kotu don yi musu shari’a.