✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama buhu 487 na lalataccen garin fulawa a Kano

hukumar ta gano hakan ne sakamakon bayanan sirrin da ta samu

Hukumar Kare Hakkin Masu Sayen Kaya ta Jihar Kano ta Kwace buhu 487 na lalatacciyar fulawa da ke jibge a wani dakin ajiye kaya da ke kasuwar Dawanau da ke jihar da ake sayar wa mutane.

hukumar ta tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwa da Kakakinta, Musbahu Aminu Yakasai, ya raba wa manema labarai a Kano ranar Talata.

Ya ce mai rikon mukamin shugabancin hukumar,  Baffa Babba Dan-Agundi Babban Mashawarcin Gwamna jihar Kano kan Inagancin kayayyaki, Alhaji Salisu Muhammad ya wakilta, ya ce wasu masu kishin kasa ne suka sanar da su a boye cewa an shigo da gurbatacciyar fulawar kasuwar ta Dawanau, kuma ana siyar da ita ga jama’a.

Ya ce jin hakan ce ta sa hukumar ta binciki fulawar ta hanyar gwada ta a dakin gwaji, ta kuma tabbatar da hakan.

Kazalika Alhaji Salisu ya ce hukumar ta kuma kwace katan-katan na lemukan sha irir-iri a kasuwar Sabon Gari da ke Kanon, wadanda su ma suka jima da lalacewa amma ake sayar wa mutane.

Hukumar ta kuma tabbatar wa da al’ummar jihar cewa ta jibge wadannan kayayyaki da ta kwace a dakin adana kayayyakinta, tare da jan hankalin al’umma da su rika duba kwanan watan lalacewar kayayyaki kafin su saya.