✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama dan bindiga an kwace makaminsa a Kaduna

’Yan sandan sun kwace bindiga kirar AK-47 da harsasai 29 a hannun dan ta’addan

’Yan sanda sun cafke wani dan bindiga da ya addabi mazauna kauyen Mariri da ke yankin Saminaka a Karamar Hukumar Lere ta Jihar Kaduna.

’Yan sandan sun kuma yi nasarar kwace bindiga kirar AK-47 da harsasai 29 a hannun dan ta’addan, wanda kuma dan kauyen ne.

Kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ya ce wanda ake zargin ya amsa cewa shi dan wani gungun ’yan bindiga da satar shanu ne da suka addabi yankin.

Jalige ya ce an cafke dan bindigar ne bayan samun bayanan sirri kan jigilar haramtattun makamai a kauyen Mariri.

“Shi ne Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, CP Yekini Ayoku, ya sa a tare yankin, wanda ya kai ga cafke su rana 7 ga Yuli, 2022 da misalin karfe 6 na yamma,” inji shi.

A cewarsa, Kamishinan ’Yan Sandan ya yi kira ga jama’ar yankin da su ci gaba da ba wa jami’an tsaro muhimman bayanan sirri domin dakile duk wata barazanar tsaro a fadin jihar.