✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama dan Najeriya da miyagun kwayoyi na N18m a Indiya

An kama mutumin ne mai suna Nnamdi Samuel a birnin Mumbai

Jami’an tsaron kasar Indiya sun kama wani dan Najeriya mai suna Nnamdi Augustine Samuel bisa zarginsa da safarar miyagun kwayoyin da darajarsu ta kai Naira miliyan 18.

A cewar jaridar Times of India, jami’an tsaron kasar ne suka kama shi karkashin dokar NDPS ta kasar a kusa da titin Dockyard da ke Mumbai ranar Lahadi.

Sashen Yaki da Miyagun kwayoyi na Rundunar ’Yan Sanda na birnin Mumbai ya kama mutumin mai shekara 36 ne da kwayoyin da suka kai Naira miliyan 18 din.

Bayan gudanar da bincike dai, hukumomin sun gano giram 61 na kwayar mephedrone da kuma giram 154 na methamphetamine, wadanda darajarsu ta kai ta kudin.

Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar, Prakash Jadhav, ya ce an kama Nnamdi ne a shekarar 2018 kan rawar da ya taka wajen wani hari da aka kai wa jami’an ’yan sandan kasar.

A cewarsa, Nnamdi ya je Indiya ne a shekarun baya, kuma an kama shi ne tare da wasu ’yan Najeriya su bakwai da haramtattun kayayyaki da dama.

Prakash ya ce yanzu haka ana ci gaba da bincike a kan lamarin ofishin ’yan sanda na Byculla da ke kasar.