✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama dan shekara 4 da bindiga makare da harsasai a makaranta

Bindigogi miliyan 400 ne ka yawo a hannun mutane a Amurka, wanda ya zarce yawan al'ummar kasar.

Wani yaro mai shekara hudu ya je makaranta dauke da bindigar gaske, makare da albarusai a cikinta a Jihar Texas ta kasar Amurka.

Ganin karamin yaron da bindigar dai sa ya cikin mutane ya duri ruwa gami da fargabar yiwuwar bude wuta a makarantar, matsalar da ke yawan aukuwa a makarantun kasar a baya-bayan nan.

Sanarwar da ’yan sanda suka fitar ta ce a ranar Alhamis ne wani jami’insu da ke aiki a makarantar ne ya gano bindigar a hannun yaron a makarantar da ka yankin Corpus Christ.

Sanarwar ta ce, duk da cewa dan sandan da ya gano yaron ba ya ya bakin aiki lokacin jami’in ya yi nasarar kwace bindigar.

Daga nan sai ya, “Ya bukaci a kawo dauki, domin an gano wani yaro mai shekara hudu dauke da bindiga a harabar makarantar.

Wannan lamari dai  ya auku ne kwana biyu kacal bayan an gano wani yaro mai shekara bakwai dauke da bindiga a wata makaranta a Jihar Arizona ta kasar.

Hakan kuna na zuwa ne a daidai lokacin da ake kammala darussan bayan hutu a kasar.

Daga baya an gano cewa bindigar mahaifan yaron ne ya dauko zuwa makarnta, har aka tsare mahaifinsa.

A halin yanzu dai ana tuhumar mahaifin, wanda shekarunsa 30 da laifin barin yaro ya dauki makami da kuma watsi da dansa gami da jefa rayuwarsa cikin hadari.

Bindigogi akalla miliyan 400 ne ka yawo a hannun mutane a kasar Amurka, adadin da ya zarce na yawan al’ummar kasar.

A baya-bayan nan dai ana yawan samun hare-hare da bindiga a makarantun kasar Amurka, inda a ranar 19 ga watan Mayu aka kashe kananan yara da malamansu biyu a wata makarantar firamare da ke Uvalde, a JiharTexas.

Ko a ranar Litinin din makon da muke ciki, ’yan sanda sun gano wani dalibi mai shekara bakwai dauke da bindiga, amma babu harsashi a cikinta da ya sanya a cikin jakarsa, a garin Cochise, da ke jihar Arizona.

Bayan sanarwar aukuwar lamarin ne mahaifin yaron ya je gida ya bincika, inda ya gano cewa an dauke bindigarsa.

Daga baya an gano daya bindigar mahaifin an boye ta a ginin ofishin gudanarwar makarantar su yaron.

Iyayen sun bayyana wa ’yan sanda cewa a iya saninsu sun boye bindigar a wurin da yaro ba zai iya kaiwa ko ya dauka ba, amma sun yi mamakin yadda dan aji biyun ya iya daukar ta har ya je da ita makaranta.

Yanzu dai yaron na fuskantar hukunci bisa dokar hukunta laifukan kananan yara.