✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama gungun ’yan bindiga a hanyar kasuwa

Bata-garin za su je cin kasuwar kauye ne suka fada komar ’yan sanda.

’Yan sanda sun kama gungun wasu ’yan bindiga a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa cin kasuwar kauye a Jihar Neja.

’Yan bindigar su hudu, dauke bindigoginsu sun shiga hannu ne bayan sun fada komar ’yan sandan Rundunar Operation Puff Adder 11 da ke Babban Ofishin  a yankin Kagara na Jihar Neja.

Kakakin ’yan sandan Jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya ce, “’Yan bindigar da shekarunsu 20 zuwa 21 ne, ’yan asalin kauyen Garun-gabas ne da ke Karamar Hukuamr Rafi ta Jihar Neja”.

Ya ce an kwace bindigogi kirar gida guda biyu a hannunsu a lokacin da suke hanyarsu ta zuwa cin kasuwar kauyen na Garun-gabas.

“Da aka titsiye su, sun fallasa wasu ayyukan satar shanu da suka yi a kauyukan Garun-gabas da Garun-dangana da yankunan da ke makwabtaka da su a Karamar Hukumar ta Rafi”.

DSP Abiodun ya kara da cewa Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta kuma cafke wani Jamilu Ibrahim wanda aka fi sani da suna “Gerald”  kan kashe wani Alhaji Samaila Isyaku a kauyen Tungar-bako a lokacin wani gangamin yakin neman zaben shugaban karamar hukuma a garin Kagara town.

A cewarsa, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Neja, Monday Bala Kuryas, ya jinjina wa jami’an Rundunar kan namijin kokarin, sannan ya bukace da su kar su gajiya, yana mai kira ga al’umma da su taimaka musu da bayanai kan duk wanda ba su amince da take-takensa ba, domin dakile ayyukan miyagu a jihar a kan kari.

Kwamishinan ya kuma ba da umarnin yin cikakken bincike kan bata-garin domin gurfanar da su a gaban kotu.

A watan Yulil ’yan sanda sun kashe ’yan bindiga 10 a wani dauki-ba-dadi da suka yi a kauyen Kundu da ke Karamar Hukumar ta Rafi.

Kananan Hukumomin Rafi da Munya da  Shiroro da kauyukan da ke makwabtaka da su sun sha fama da hare-haren ’yan bindiga, masu garkuwa da dalibai da matafiya da kuma sace dabbobi.

A baya-bayan nan gwamnatin jihar da hadin gwiwar hukumomin tsaro da ’yan banga sun matsa kaimi a Karamar Hukumar Rafi, domin dakile ayyukan maharan.