✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama hadimin wani Gwamnan Najeriya da laifin zamba a Amurka

Mista Rufai ya aikata makamancin wannan laifi a wasu jihohin Amurka shida.

Wani dan siyasar Najeriya mai suna Abidemi Rufai, ya shiga hannun mahukuta a kasar Amurka bisa zarginsa da aikata laifin zamba ta hanyar satar bayanan mutane sama da dari.

Mutumin wanda babban hadimi ne ga Gwamna Dapo Abiodun na Jihar Ogun, ya shiga hannu ne a filin tashi da saukar jiragen sama na John F. Kennedy yayin da yake yunkurin barin Amurka zuwa Amsterdam, babban birnin kasar Netherlands.

Mista Rufai mai shekaru 42, ana zarginsa da satar bayanan mazauna Washington 100 a tsakanin watan Maris zuwa Agustan shekarar 2020.

Mahukunta sun ce an aika sama da Dala 288,000 zuwa wani asusun bankinsa bayan ya rika yaudarar mutane da wani adireshin aika sakonni ta yanar gizo wanda aka sanya wa matakan tsaro da wasu na’urori da ba za su gane ba.

A Juma’ar da ta gabata ce kuma aka zargi Mista Rufai da laifin satar sama da Dala dubu dari uku da hamsin na kudaden rage radadin talauci a Ma’aikatar Ayyukan Yi ta Jihar Washington.

Baya ga Washington, Mista Rufai ya aikata makamancin wannan laifi a Jihohin Hawaii, Wyoming, Massachusetts, Montana, New York da Pennsylvania.

Wata sanarwa da Ma’aikatar Shari’ar Amurka ta fitar ta ce ana sa ran za a gurfanar da shi gaban Kuliya a ranar Laraba, inda za a yi yanke masa hukuncin cin sarka na shekara 30 a gidan kaso.

Tuni dai Gwamnatin Jihar Ogun ta dakatar da Mista Rufai daga mukaminsa kamar yadda sashen Hausa na BBC ya ruwaito.