✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama hafsan dan sanda yana shan tabar wiwi a bakin aiki

Hoton dan sandan yana zukar tabar wiwi a bakin aiki ya karade kafofin sada zumunta

Sagiru Kano Saleh,

7th March, 2022.

Ag. President,

MTL Cooperative Society.

Dear sir,

WITHDRAWAL OF MEMBERSHIP

I hereby wish to inform you of the immediate withdrawal of my membership of the MTL Cooperative Society, for personal reasons.

I also seek the withdrawal and transfer of my contributions so far to my bank account thus:

  • Account number: 0000704519
  • Bank: Jaiz Bank
  • Account name: Sagir Kano Saleh

By this, further withdrawals from my monthly salary in respect of the cooperative should be discontinued, please.

Yours faithfully,

Sagir Kano Saleh.

An tsare wani hafsan dan sanda da aka kama yana zukar tabar wiwi a bainar jama’a a bakin aikinsa.

Dan sandan mai mukamin ASP, Babatunde Adebayo, ya shiga hannu ne bayan wani hotonsa da aka dauka a fakaice ya karade gari inda ya mola tabar wiwi yana kuma busa hayakinta a wurin wani taro.

A ranar Lahadi ne dai aka baza hoton hafsan dan sandan a kafofin sada zumunta, yana shan tabar wiwi, a tare da hoton aka rubuta “Hafsan dan sandan Najeriya yana shan tabar wiwi a bakin aiki a yankin Ijora, Jihar Legas.”

Wata sanarwa da Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Legas ta fitar ta ce ASP Adebayo wanda ke aiki da ofishin ’yan sanda da ke Shogunle a jihar ya shiga hannu kuma zai fuskanci hukunci bisa dokar aikin dan sanda.

Kakakin rundunar, SP Benjamin Hundeyin, ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Legs, Abiodun Alabi, ya ba da umarnin a fara gudanar da bincike a kan ASP Adebayo ba tare da bata lokaci ba domin ya girbi abin da ya shuka daidai da matsayinsa.

“CP Alabi ya kuma gargadi kanana da hafsoshin ’yan sanda su guji duk wani abu na rashin da’a ko saba dokokin aikinsu, domin duk wanda aka kama zai yaba wa aya zaki,” inji sanarwar.