✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama ‘likitan bogi’ kan taimakon ’yan bindiga

Mazauna sun ce rabon da a gan shi tun jajibirin garkuwa da Daliban Kankara.

’Yan sanda sun cafke wani likitan bogi da ake zargin yana taimaka wa ’yan bindigar da aka yi wa rauni magani a cikin daji

Mazauna garin Kankara sun ce wanda ake zargin ya yi batar dabo daga garin tun ranar da aka sace Daliban Kankara a watan Disamban 2020. 

Ba a sake jin duriyar mutumin wanda dan aslin Jihar Kogi ne ba sai ’yan kwanakin nan, lamarin da ya kara karfin zargin da suke masa na alaka da ’yan bindiga. 

Runduar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta gabatar da shi ga manema labarai da maraicen Talata.

Ko da aka titsiye shi kan a ina ya yi karatun aikin likitan, sai ya buge da kame-kame a gaban ’yan jarida. 

Ya kuma gaza yin cikakken bayani a kan wasu magungunan da aka kama shi da su da ake zargin da su yake yi wa ’yan bindiga magani. 

Amma wanda ake zargin ya ce ’yan bindiga ne suka sace shi, inda ya shafe kwana shida a hannunsu kafin a biya kudin fansa su sako shi. 

Kakakin ’yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isa, ya ce za su ci gaba da bincike kan wanda ake zargin.