✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama ma’aikatan lafiya 7 kan zargin karkatar da gidajen sauro a Gombe

Yanzu haka dai mutanen na tsare a hannun 'yan sanda.

Jami’an tsaro a Jihar Gombe sun cafke ma’aikatan lafiya bakwai kan zargin karkatar da gidajen sauro sama da 5,450 a Kananan Hukumomin Billiri da Kwami da ke Jihar.

A makon day a gabata ne Gwamnan Jihar, Inuwa Yahaya ya kaddamar da rabon gidajen sauroN masu dauke da magani miliyan biyu a Jihar kyauta, sai ga shi an zargi wasu ma’aikatan da karkatar da su zuwa kasuwa.

Wani binciken da wakilin mu ya gudanar a birnin Gombe ya gano cewa mafi yawancin magidanta a garin sun koka kan yadda aka tsallake gidajen su ba tare da an basu gidan sauron ba.

Binciken, har ila yau ya gano cewa masu rabon gidajen sauron suna tsallake wasu gidaje ne a lokacin aikin rabon saboda yin hakan zai basu damar tarawa da yawa dan karkatar da shi.

Wani magidanci a Gombe da ya bukaci a sakaya sunansa ya zargi wasu daga cikin masu aikin rabon gidan sauron ne da hada baki da ’yan kasuwa wajen karkatar da gidan sauron don sayarwa, duk kuwa da gwamnati ta ce a raba kyauta.

“Ni ba a kawo min gidan sauro a gidana ba kuma duk layin unguwar mu babu wanda aka ba wa,” inji magidancin.

Da wakilin mu ya tuntubi Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwar Jihar Gombe, Alhaji Sunusi Abdullahi Mai Rediyo, ya tabbatar da zargin da ake yiwa wasu mambobin nasu na sayen gidajen sauron.

Sai dai ya ce kungiyarsu za ta dauki matakin doka kan duk wanda aka samu da laifin sayen gidan sauron.

Ya kuma ce za su cire hannunsu a kungiyance kan duk wanda aka samu da laifin saboda yin hakan zagon kasa ne ga gwamnati.

Wakilin mu ya shaida mana cewa ’yan sanda sun kama kayan da aka karkatar din kuma wata majiya daga rundunar ta tabbatar da cewa yanzu haka suna  gudanar da bincike a kai.

A bangaren ’yan kwamitin rabon gidan sauron kuwa, Shugaban kwamitin, kuma Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dokta Habu Dahiru, ya ce jami’an tsaro sun yi nasarar cafke jami’an Hukumar Kula da Lafiya a mMatakin Farko daga Kananan Hukumomin Kwami da Billiri, kan zargin karkatar da gidan sauron.

Dokta Habu Dahiru ya kara da cewa kwamitin dake da alhakin Sanya ido kan rabon gidan sauron domin ganin cewa gidan sauron ya isa ga dukkanin al’ummar jihar ne ya  kame mutanen da ake zargin.

Ya kara da cewa tuni jami’an tsaron suka dakatar da motar da ke dauke da gidan sauran domin aiwatar da bincike, sannan suka gano akwai hannun ’yan kasuwa dumu-dumu a badakalar.

Kwamishinan ya kuma ce nan take suka tisa keyarsu zuwa hedkwatar ’yan sanda domin ci gaba da gudanar da bincike.

 Dokta Habu Dahiru ya  jinjinawa dukkan bangarorin jami’an tsaro, musamman  ’yan sanda da na DSS da NSCDC dangane da irin rawar da suka taka wajen gano gidan sauro da akayi yunkurin karkatarwar da nufin sayarwa ’yan kasuwa.

Har ila yau Kwamishinan ya yi kira ga al’ummar Jihar da su ci gaba da dafawa yunkurin gwamnati ta hanyar sanya ido  wajen ganin ba a karkatar gidajen sauron ba.