Daily Trust Aminiya - An kama magidancin da ya daba wa matarsa wuka a Anambra
Subscribe

An kama magidancin da ya daba wa matarsa wuka a Anambra

Ana zargin wani magidanci mai matsaikatan shekaru, Kingsley Igwe, da kashe matarsa da wuka a yankin Nise na Karamar Hukumar Akwa ta Kudu a Jihar Anambra.

Mutumin da ake zargi kamar yadda wani shaidar gani da ido ya bayar da tabbaci a kan lamarin, ya daba wa matarsa mai shekara 31 wuka, lamarin da ya gadar mata da raunuka har ya kai ga mutuwarta.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar CSP Haruna Muhammad ya bayar da tabbaci kan aukuwar lamarin da kuma shigar wanda ake zargi hannu.

A cewarsa, “Da misalin karfe 4 na Asubahin ranar Alhamis 4 ga watan Maris ne jami’an rundunar ’yan sanda suka kama wani Kingsley Igwe mai shekara 35 mazaunin unguwar Otigba, wanda ake zargi ya kashe matarsa da wuka.”

Ya ce nan da nan jami’an suka hanzarta kai dauki wurin da abin ya faru, inda suka mika matar da aka dabawa wuka zuwa wani babban Asibiti kuma wani likita ya tabbatar ta riga mu gidan gaskiya.

Sai dai an killace gawarta a dakin ajiyar gawawwaki na asibitin domin fadada bincike a kan musababbin mutuwarta.

Ya ci gaba da cewa, an kuma gano wukar da aka yi aika-aikar da ita wacce za a gabatar a matsayin shaida a gaban Kotu.

Kazalika, ya ce Kwamishinan ’yan sandan jihar Monday Bala Kuryas, ya umarci a mika lamarin zuwa ofishin binciken miyagun laifuka da ke Awka domin fadada bincike.

More Stories