✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama magidanci ya kulle matarsa shekara 4 a keji

A ciki take bayan gida da fitsari, sannan biredi kadai ake ba ta a matsayin abinci.

Wata mata mai suna Gladys na jinya a asibitin Orerokpe da ke Jihar Delta, bayan mijinta ya kulle ta a cikin keji a daki shekara hudu kan zargin ta da maita.

Harrison Gwamnishu, wanda shi ne ya fallasa abin da ke faruwa, ya bayyana wa Aminiya yadda mijin Gladys ya rufe ta cikin wani keji a gidansu sakamakon yana zarginta da maita.

An ceto Gladys ce daga kejin da aka kulle ta a tsakar gidan, kuma an bayyana cewa a cikin kejin take bayan gida da fitsari, haka kuma biredi kadai ake ba ta a matsayin abinci.

A halin yanzu dai Gladys na asibitin Orerokpe inda a nan ne take jinya tare da karbar magani.

Harrison ya bayyana cewa Gladys na da ’ya’ya takwas, haka kuma ta haifi uku daga cikinsu yayin da take kulle a cikin kejin.

“Ita asalin ’yar garin Ozoro ce daga Jihar Delta kuma da alamu ta kai shekara 40.

“A yanzu ba ta cikin hayyacinta da za ta iya magana domin tun jiya ba ta ce komai ba.

“Amma muna so mu kai ta zuwa wani asibiti domin duba lafiyarta. A halin yanzu mijinta na wurin ’yan sanda”, inji shi.

Harrison ya kara da cewa, a halin yanzu Ma’aikatar Harkokin Mata ta Jihar Delta na kula da ’ya’yan matar saboda kanana ne, tun daga babban zuwa karamin.

Ya ci gaba da cewa yayin da ake kula da mahaifiyar yaran kafin ta murmure, za su san yadda za a yi a kai wannan lamarin zuwa ga sashen da ke binciken laifuka a jihar wato State CID.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sanda reshen Jihar Delta, Onome Umukoro ya tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin, inda ya ce tuni aka kama mijin Gladys domin kaddamar da bincike a kansa.

Umukoro ya bayyana cewa, mijin ya shaida musu wai matar na da tabin hankali ne shi ya sa kuma ana zarginta da maita amma hakan ya sa yake tare da ita.

Ya ce, ya kai ta wurin masu maganin gargajiya daban-daban amma lamarin ya gagara.

Ya kuma ce ya kai ta wurin danginta amma sun yi watsi da ita, inda suka ki karbar ta, wanda hakan ya sa ya dawo da ita gida domin ya ci gaba da hukuri da ita.