✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mahaifi kan zargin sayar da ’ya’yansa saboda bashi

Ya yi niyyar sayar da ’ya’yan ne saboda tsananin talaucin da yake fama da shi.

Jami’an Hukumar Tsaro ta Civil Defence a Jihar Akwa Ibom, sun cafke wani mutum yana kokarin sayar da ’ya’yansa biyu saboda kantar bashi da ta yi masa katutu. 

Ana zargin mutumin da hada baki da matarsa wajen sayar da ’ya’yansu guda biyu biyu mata a kan Naira 700,000 domin ya biya bashi.

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Umana Ukeme ya fitar ranar Laraba, ta ce mutumin ya shiga hannu ne a Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom.

Umana Ukeme  ya ce mutumin wanda ke ke rayuwa a Kasar Kamaru, ya shiga hannu ne tare da mai dakinsa a ranar 15 ga watan Nuwamba, bayan bincike sirri ya bankado yunkurinsa na sayar da yaran mata biyu.

Jami’in na hukumar NSCDC ya ce daya daga ’ya’yan mutumin akwai mai shekarun haihuwa shida sai kuma karamar mai shekaru hudu.

Sanarwar ta ambato mutumin mai shekara 40 da ake zargi yana cewa ya yi niyyar sayar da ’ya’yansu ne saboda tsananin talaucin da yake fama da shi.