✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mahaukaciya da bindigogi a Legas

An kona mahaukaciyar karyar bayan an kama ta da sassan jikin dan Adam.

Fusatattun matasa sun kona wata mahaukaciya kurmus bayan an same ta da bindigogi kirar AK 47 guda hudu.

Jama’ar unguwa sun ce an kuma gano sassan jikin dan Adam a tare da mahaukaciyar karyar da ke zamaa karkashin wata gada.

Ana kuma zargin bindigogin da aka kama a wurinta na ’yan fashi ne da ke ba ta ajiya.

Dubun matar wadda ke yin shiga a matsayin mahaukaciya ya cika ne a safiyar Litinin a unguwar Abule-Ado da ke Badagry a Jihar Legas.

Wani matashi da ke zaune a daura da yankin mai suna Abdullahi Alkanawiy, ya shaida wa Aminiya cewa a lokacin da lamarin ya faru ya zo wucewa ta wajen a mota sai ya tarar an banka wa matar wuta.

“Na tsaya na tambaya sai ake fada mini cewa an same ta da bindigar AK 47 guda hudu; Matar sananniya ce, duk wanda yake wucewa ta wajen zai rika ganin ta a karkashin gada, da ka gan ta ka ga mahaukaciya,” inji shi.

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin kakain Rundunar ’Yan Sanda na Jihar Legas, Olamuyiwa Adejobi, amma bai daga waya ba, bai kuma amsa rubutaccen sakon da wakilinmu ta tura masa ba.