✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mai garkuwa ya je banki ciro kudin fansa

Mai asusun ajiyar da aka yi amfani da shi kuma yana cikin tsaka mai wuya.

’Yan Sanda sun yi caraf da daya daga cikin wadanda ake zargi da yin garkuwa da mutane ya je karbar kudin fansa ta banki a Abuja.

Bayan an cafke mai garkuwar, mutumin da ke da asusun bankin da masu garkuwar suka yi amfani da shi ya dauki lauyan mai kare shi don ya tabbatar da cewa ba shi da hannu a lamarin.

Aminiya ta kawo rahoron yadda mijin daya daga cikin wasu mata da aka yi garkuwar da su ya tura wa masu garkuwar kudin N500,000 a cikin wani bankin Access Bank da sunan Badawi Abba Enterprise.

Wakilinmu ya ziyarci ofishin ’yan sanda da ke  Suleja, Jihar Neja a ranar Alhamis don jin inda aka kwana inda ya samu ba a tsare mai asusun bankin ba, wanda ake zargi da garkuwar kuma ba a sa masa ankwa ba.

’Yan sanda sun nemi a sasanta

Wakilinmu ya ce rundunar ’yan sandan kuma gayyaci mijin domin rubuta bayani a kan lamarin.

Bayan haka ne Kwamandan Yankin Suleja ya umarci dan wani dan sanda mai suna Insp. Idris da dangin wadanda ake zargin da kuma lauyan mai asusun bankin su sasanta da mijin matar, amma mijin ya ce ba batunsa ba ne saboda haka babu abin da za a sasanta.

Bangarorin, ciki har da ’yan sanda, sun yi ta rarrashin mijin matar a kashe maganar, suna cewa, “Hau ce ta hau kan wanda ake zargin”.

Duk da haka mijin matar ya ce ’yan sanda su bar wanda ake zargin ya kawo sauran wadanda ake zargi da ya ba su kudin bayan ya cira a baki.

Da yake magana, mai asusun bankin, ya ce bai taba sanin komai game da lamarin ba sai da bankin nasa — Access — ya tuntube shi don neman bayani kan abin da ke faruwa, nan take ya tuntubi lauyansa.

Ya ce zai iya tuna cewa a watan Yuni ya bayar da lambar ajiyarsa ga wani mai harkar tura kudi ta POS a kusa da shagonsa a Kasuwar Ibrahim Badamasi Babangida da ke Suleja, Jihar Neja.

Wani jami’in dan sanda da yake zantawa da wakilinmu bisa sharadin ba za a bayyana sunansa ba, ya ce a baya sun gano batutuwan satar mutane amma wasu manyan ’yan siyasa suna rufe maganar.

Jami’in dan sanda mai binciken lamarin, Insp. Idris ya fada wa wakilinmu ta wayar tarho cewa za a tura batun zuwa Sashen Yaki da Satar Mutane a Minna, babban birnin Jihar Neja.

Mun tuntubi kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Abuja, Maryam Yusuf, amma ta ce lamarin yana karkashin ikon Jihar Neja, sannan ta tura wakilinmu ga kakakin ’yan sanda na Jihar Neja, Wasiu Abiodun.

Abiodun, a zantawarsa da wakilin namu ta wayar tarho ya yi alkawarin waiwayar sa ya gama bincikensa daga jami’ansu da ke Suleja.