✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama malami kan zargin lalata da dalibarsa a Adamawa

Malamin ya yaudari dalibar zuwa wani kango.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Adamawa ta cafke wani malami mai shekaru 52 kan zargin lalata da dalibarsa.

Ana zargin malamin da yi wa wata dalibar mai shekara 13 fyade a garin Sangere Jabbi Lamba da ke Karamar Hukumar Girei.

Wannan dai yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ya fitar a ranar Talata.

Sanarwar ta ce tun a ranar 15 ga watan Nuwamba ne wanda ake zargin ya yaudari yarinyar zuwa wani kango wanda a nan ya yi lalata da ita.

SP Nguroje ya ce mahaifiyar yarinyar ce ta kai rahoton lamarin ga hedikwatar ‘yan sanda da ke yankin Jabbi a Lamba.

Kwamishinan ‘Yan Sanda Sikiru Akande, ya umarci jami’in da ke kula da sashen manyan laifuka da suka gudanar binciken tare da tabbatar da an gurfanar da malamin da ake tuhuma a gaban kotu.

Akande ya shawarci iyaye da su rika lura da ‘ya’yansu, musamman mata, saboda yawaitar masu lalata yara.