✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama malamin Islamiya ya yi wa dalibarsa fyade

Dubun wani malamin Islamiyya ta cika bayan ya yi wa dalibarsa alkawarin cire mata ciki, amma ya buge da yi mata fyade. Dalibar mai shekara…

Dubun wani malamin Islamiyya ta cika bayan ya yi wa dalibarsa alkawarin cire mata ciki, amma ya buge da yi mata fyade.

Dalibar mai shekara 15 da aka sakaye sunanta, ta ce a ranar 25 ga watan Agusta, 2020 wani matashi mai shekara 20 ya yi mata fyade a yankin Imedun-nla da ke unguwar Ibafo a Jihar Ogun.

Hakan ne ya sa ta zuwa wajen malaminsu na makarantar Islamiyya, ta bayyana masa halin da ake ciki tare da neman taimakonsa; Sai ya kada baki ya ce mata tunda fyade aka yi mata akwai tabbacin ta dauki ciki don haka zai taimaka ya cire mata cikin.

Ta ce a maimakon ya cire mata cikin da ya ce ta dauka, sai shi ma ya yi mata fyade, sannan ya saka mata wani abu mai kaifi a cikin farjinta, ya yi mata rauni.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Aminiya cewa Rundunar ta kame wadanda ake zargi da yi wa dalibar fyade su biyu.

“Bayan dalibar ta yi karar wadanda ake zargin, sai Baturen ’Yan Sandan yankin, SP Bala Yakubu ya jagoranci jami’ansa suka yi nasarar kama wadanda ake zargin a ranar 28 ga watan Agustan 2020.

“Sun amsa laifin da ake zargin su da aikatawa, kana ana ci gaba da bai wa dalibar kulawa a asibiti”, inji shi.

Abimbola Oyeyemi ya ce ana ci gaba da bincike, za kuma a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu.