✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama masara da gero masu dauke da guba a Kano

Direban mota daya da abokin mai kayan hatsin sun shiga hannun hukuma.

An kama masara da gero masu dauke da guba cikin tireloli da aka yi fasakwaurinsu zuwa kasuwar hatsi ta Dawanau da ke Jihar Kano.

Hukumar karbar korafi da yaki da rashawa ta Jihar Kano ta kwace kayan hatsin ne bayan ta kama motocin da ke dauke da su a wani samame da ta kai kasuwar.

“Bisa dukkan alamu masarar tana dauke da guba. Mutanen suna gauraya masarar mai guba ce da mara guba su zuba a buhuna su kai kamfani a nika hatsin a rika sayar wa mutane da garin girkin.

“Haka mutane ke ta cin irin wannan gubar ba su sani ba,” inji mukaddashin shugaban hukumar, Barista Mahmoud Balarabe.

Da yake baje kolin hatsin mai dauke da guba a ranar Juma’a, shugaban hukumar ya ce bayan samun rahoto game da ayyukan bata-garin ne jami’an hukumar suka kai samame suka kama kayan.

Mahmoud Balarabe, ya bayyana cewa irin wadannan hatsi masu dauke da guba na iya yaduwa har a wajen Najeriya, saboda kasuwar Dawanau ita ce kasuwar hatsi mafi girma a yankin Afirka ta Yamma.

Ya ce jami’an hukumar sun kama kayan ne a ranar Alhamis tare da direban daya daga cikin tirelolin da wani mutum wanda ya ce mai kayan  ne abokinshi.

A cewarsa, hukumarsa za ta yi wa shugabannin kasuwar tambayoyi, “Musamman shugabannin masu sayar da masara da gero don mu ji abin da suka sani game da lamarin.”

Ya kara da cewa hukumar ta tashi haikan domin ganin ta gano ta kuma kamo mai kayan da kuma dakin ajiyar da aka kai su.