✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama ‘masu fyade’ 40 a Katsina

Masu fyade guda 40 ne dubunsu ta cika a Jihar Katsina a watanni biyu da suka gabata, a yayin da matsalar ta fyade da dangoginta…

Masu fyade guda 40 ne dubunsu ta cika a Jihar Katsina a watanni biyu da suka gabata, a yayin da matsalar ta fyade da dangoginta ke kara yawaita a jihar.

Ana zargin mutum 40 din sun yi wa mata da kananan yara fyade da a wasu lokuta suka saba wa hankali a sassan jihar tsakanin watan Afrilu zuwa Yuni na shekarar 2020.

Yayin sanar da hakan, Kamishinan ‘Yan Sandan Jihar Katsina Sanusi Buba ya bukaci jama’a da su taimaka wurin samar da muhimman bayanai da za su kai ga kama masu mummunar dabi’ar domin kawo karshen matsalar.

Sai dai ya ce ana samun gagarumar nasara a yaki da rundunar ke yi da laifukan fyade a jihar.