✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama masu haramtacciyar Kwalejin kimiyyar lafiya a Neja

’Yan Sanda sun kamo wasu mutane biyu da ake zargi da bude haramtacciyar Kwalejin Kimiyyar Lafiya a Karamar Hukumar Bosso ta Jihar Neja.

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Neja, ta kamo wasu mutane biyu da ake zargi da bude haramtacciyar Kwalejin Kimiyyar Lafiya a Karamar Hukumar Bosso da ke jihar.

Kakakin Rundunar, Wasiu Abiodun ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Talata a Minna.

Abiodun ya kuma ce wadanda ake zargin na sojan gona ne a matsayin shugaba, da kuma daraktan makarantar da suka sanyawa suna Excellence College of Health.

Kafin rufe ta, Kwalejin tana da dalibai 100, wadanda kowanne ke biyan N78,000, duk shekara a matsayin kudin makaranta.

Kakakin ya kuma ce an kamo mutanen ne a ranar 9 ga watan Satumba, bayan samun bayanan sirri.

“Mutanen biyu da ake zargi sun kafa makarantar bayan fage a karamar Hukumar Bosso.

“Sun amsa da bakinsu cewa sun kafa ta tun a shekarar 2020, kuma sun fara dibar dalibai a 2021 ba tare da sahalewar kowacce hukuma ba a Najeriya.

“Sun kuma bayya cewa sun mallaki takardun bogi, da suke nunawa mutane, don samun dalibai”, in ji shi.

Abiodun ya ce daya daga cikin wadanda ake zargin dan asalin garin Enugu ne, kuma shi ke rike da matsayin Daraktanta, yake kuma kula da ayyukanta, da malamai 20 da suka dauka aiki.

Haka kuma ya ce za a gabatar da su a gaban kotu, da zarar an kammala bincike.