✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama masu sayar da kayan da Bankin Duniya ya bayar a raba wa dalibai a Kaduna

An kama su suna sayar da jakunkunan da bankin ya bayar a raba wa dalibai kyauta

An cafke wasu ‘yan kasuwa su uku a Jihar Kaduna bayan an same su suna sayar da wasu jakunkunan makaranta wanda Bankin Duniya ya bayar a matsayin gudunmawa ga Gwamnatin Jihar. 

Bankin na Duniya ya bai wa Gwamnatin Kaduna jakunkunan ne karkashin shirinsa na bunkasa sha’anin ilimi (BESDA) don raba wa daliban firamare kyauta a jihar.

Tuni aka maka wadanda ake zargin a kotun majistare bisa tuhumar sata da kuma sayen kayan sata.

Bayanan da kotun ta samu sun nuna an kama daya daga cikin wadanda ake zargin yana sayar da jakar a watan Agusta a yankin Sabon Tasha cikin Karamar Hukumar Zangon Kataf da ke jihar.

An same su ne suna sayar da jakunkunan a kan farashi tsakanin N1,500 zuwa N1,700 kowacce.

Daga bisani, kotun ta dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 28 ga Nuwamban 2022.

Sau da yawa, akan fuskanci irin wannan matsalar a cikin al’umma, inda kayayyakin tallafi da akan bayar don raba wa jama’a kyauta ba su isa gare su, ko kuma a sayar musu maimakon kyauta.

(NAN)