✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama matar dan bindiga tana safarar makamai

Matar ta amsa cewa mijinta babban dan bindiga ne kuma shi ne ya aike ta.

An kama wata mata mai shekara 27 bisa zargin yi wa ’yan bindiga safarar makamai a Jihar Katsina.

Dubun matar wadda ta ce mijinta dan bindiga ne ta cika ne a lokacin da take dauke da tsabar kudi Naira milyan biyu da dubu dari hudu da biyar a hanyarta ta zuwa cinikin makaman ’yan bindiga a jihohin Katsina da Kaduna.

Da yake gabatar da matar ranar Juma’a, kakakin ’yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isa ya ce asirinta ya tonu ne a garin Batsari tana kokarin daukar hayar babur zuwa kauyen Nahuta a ranar 25 ga watan na Yuli.

Bayanai sun nuna matar ta nuna alamun rashin gaskiya da kuma tsarguwa a lokacin da take kokarin daukar mai babur din, wanda hakan ya janyo tuhuma gare ta.

“Dubunta ya cika ne bayan an lura tana ta boye-boye a lokacin da take kokarin hawa babur din haya daga garin Batsari zuwa kauyen Nahuta,” inji SP Gambo.

Ya ce da farko matar ta nuna ba ta dauke da komai, amma da tuhumar ta yi nisa aka bincika sai aka same ta da tsabar kudaden da ake zargin ladar safarar makaman da aka yi wa ’yan bindiga ne zuwa Kaduna.

“Da aka titsiye ta sai ta amsa cewa mijinta wanda hatsabibin dan bindiga ne daga cikin yaran shugaban ’yan bindiga Abu Radda ne ya sa ta wakilce shi wurin karbo kamashon kudin daga wuirn ’yan bindiga a dajin Kaduna,” kamar yadda ya bayyana ya kara da cewa ana ci gaba da bincike.

Ya ce rundunar ta kuma cafke wani dan fashi dan asalin kauyen Kufan-Kanawa da ya addabi yankin na Batsari.

Wanda ake zargin ya ce shi da wasu mutum biyu wadanda a yanzu ake neman su ruwa a jallo, su ne suka shiga wasu gidaje a garin Fura Girke suka yi fashi tare da tafiya da wasu kaddarori.

Kakakin ya ce ana ci gaba da laluben duk wasu bata-gari, sannan ya yi kira ga jama’a da su ci gaba ba su hadin kai da goyon ta hanyar bayar da bayanan sirrin da za su kai ga kamo su.