✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama matashi da bindigogi da rigar Fulani a Kafanchan

An samu mtashin da rigar saka da aka fi sanin Fulani makiyaya na amfani da ita.

Rundunar ’yan sanda a garin Kafanchan na Karamar Hukumar Jama’a ta Jihar Kaduna, ta samu nasarar cafke wani matashi da aka samu bindigogi a motarsa.

Matashin mai suna Geoffrey Ayuba, an cafke shi ne da misalin karfe hudu na yammacin Laraba bayan ya kai gyaran motar da bindigogin ke ciki a wani garejin gyaran mota da ke garin Kafanchan.

A kan haka ne wasu suka fara nuna alamar rashin gamsuwa bayan sun lura da take-takensa, inda ba tare da wata-wata ba aka kira ’yan sanda su ka yi caraf da shi.

Bayan wani dan takaitaccen bincike ne ’yan sandan suka gano bindiga kirar AK 47 guda daya, da wasu bindogogi kirar gida guda biyu da kuma rigar saka da aka fi sanin Fulani makiyaya na amfani da ita.

Wani jami’in tsaro da ya bukaci a sakaye sunansa, ya ce ana ci gaba da bincike a kan matashin da ya bayyana cewa shi mutumin Unguwar Rimi Bajju ce da ke makwabtaka da garin Kafanchan.

Geoffrey Ayuba a jikin motarsa da ya kai gyara
Geoffrey Ayuba rike da bindigar AK-47 da aka samu a motarsa
Bindigar AK-47 da aka samu a motarsa
A nan ma matashin yana rike da bindigar AK-47 da aka samu a motarsa
Bindiga da alburusai da aka samu a motarsa

A cewar jami’in, ana gudanar da binciken ne don jin inda matashin ya samu makamin da ake zargin yana safararsu.