✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama matashi sa’o’i bayan fitowarsa daga gidan yari

Wata kungiya ce ta biya masa tarar da aka yanka masa.

Wani matashi a Jihar Legas ya fada a komar ‘yan sanda jim kadan bayan an sako shi daga gidan kaso.

Ana zargin matashin da satar wasu kayayyakin wata mota da ke ajiye a wajen gyara.

Cikin sanarwar da ya fitar ranar Alhamis, mai magana da yawun ‘yan sandan yankin, SP Benjamin Hundeyin ya ce, an cafke matashin ne bayan sa’o’i hudu da sako shi daga kurkuku.

“An damke wanda ake zargin ne ranar Asabar bayan fitowa daga kurkuku inda ya shafe wata daya kan laifin satar fetur.

“Wata kungiya mai zaman kanta ce ta taimaka wajen fito da shi daga gidan yarin ranar Juma’a bayan ta biya masa tarar da aka yanka masa,” inji shi.

(NAN)