✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mota dauke da tabar wiwin N30m an Kano

Jami’an Hukumar Kula da Sufru ta Jihar Kano (KAROTA) sun tsare wata mota makare da tabar wiwi da kudinta ya kai Naira miliyan 30. Kakakin…

Jami’an Hukumar Kula da Sufru ta Jihar Kano (KAROTA) sun tsare wata mota makare da tabar wiwi da kudinta ya kai Naira miliyan 30.

Kakakin Hukumar KAROTA, Nabulisi Abdullahi, ya ce an kama direban motar kirar Golf, wadda a cikinta aka samu curi 172 na tabar wiwin da kudinta ya kai N30m a hanyar Gwarzo zuwa Kano.

“An cafke motar da misalin 3:30 na dare ranar 20 ga Janairu, inda aka kama direban a hanyar Gwarzo zuwa Kano, sauran kuma wadanda da ake zargin su ne masu kayan sun ranta a na kare,” inji shi.

Nabulisi ya ce KAROTA ta damka motar ga Hukumar NDLEA mai yaki da sha da fataucin miyagun kowayoyi domin zurfafa bincike.

Da yake kira ga al’umma da su taimaka da rahoton masu safarar miyagun kwayoyi, Nabulisi ya ce hakan zai taimaka wajen cafke gungu -gungu da daidaikun masu aikata miyagun laifuka a jihar Kano.

Kakain NDLEA an Jihar Kano, Sani Danwawo, ya tabbatar da kamen ya kuma ce an hannanta wa NDLEA tabar wiwi din da aka kama.

Danwawo ya ce hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen aikinta da yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi a jihar.