✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mutanen da suka kai sabon hari a Jos

Mutum 10 sun shiga, ana kuma farautar sauran bayan kazamin harin.

Hukumomi a Jihar Filato sun cafke akalla mutum 10 da ake zargi da sabon harin da aka kai a garin Jos a daren Talata zuwa wayewar garin Laraba.

Gwanman Filato, Simon Lalong ne ya sanar da kame mutanen a yayin da yake Allah wadai da harin da aka kai a kauyen Yelwa Zangam da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa ta Jihar.

Lalong ya bayyana harin a matsayin dabbanci, ya kuma umarci jami’an tsaro da su tabbata sun gano sun kuma kamo sauran masu hannu a harin domin su fuskanci hukuncin laifin da suka aikata.

Sanarwar da Daraktan Yada Labaran Gwamnan, Makut Simon Macham, ya fitar ta ce: “Lalong ya fusata da harin da rahotannin suka tabbatar an tsara shi sosai ta yadda aka lalata gadar zuwa kauyen domin hana jami’an tsaro isa wurin a lokacin harin.”

Kakakin ’yan sandan Jihar Filato, ASP Ubah Gabriel, ya tabbatar da harin, amma ya ce sai nan gaban zai fitar da sauran bayanai.

Amma wani mazaunin kauyen, Yakubu Bagudu, ya shaida wa wakilinmu cewa maharan sun kashe akalla mutum 30 a harin da aka kai da tsakar dare.

Yakubu ya kara da cewa maharan sun kuma cinna wa wasu daga cikin gawarwakin wuta sun kuma kona gidaje.

Sabon harin an kai shi ne kasa da kwana 10 bayan fusatattun ’yan kabilar Irigwe a jihar sun tare wasu motocin matafiya Fulani suka yi wa mutum kusan 30 a cikinsu kisan gilla tare da jikkata wasu da dama.

Lamarin ya nemi ya fantsama zuwa sauran sassan jihar, inda aka yi yunkurin kai harin ramuwar gayya, amma gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita.