✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mutum 2 da suka yi garkuwa da ba’Amurke a jihar Sakkwato

Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta cafke wasu mutum biyu daga cikin gungun masu garkuwa da mutane a tsakanin Nijar da Najeriya da suka sace wani…

Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta cafke wasu mutum biyu daga cikin gungun masu garkuwa da mutane a tsakanin Nijar da Najeriya da suka sace wani Ba’Amurke, Philippe Nathan Walton.

Sanarwar da Rundunar ta fitar cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter ta bayyana sunayen matasan biyu da suka shiga hannunta tun a ranar 25 ga Nuwamba; Aliyu Abdullahi mai shekaru 21 da Aliyu Umaru mai shekaru 23 – wanda dukkaninsu ’yan asalin jihar Sakkwato ne.

A ranar 28 ga watan Oktoba ne aka sace Mista Walton a wata gonarsa da ke kauyn Masalata a Jamhuriyyar Nijarr, inda a ranar 31 ga watan Oktoba kuma wasu Jami’an Tsaro na musamman na Kasar Amurka suka ceto shi a jihar Sakkwato.

Ababen zargin biyu na daga cikin gungun masu satar mutane da neman kudin fansa da ya kunshi mutum goma sha biyar, da suka hada da ’yan Najeriya da Nijar, wadanda Barte Dan Alhaji da Dan Buda ke jagorantarsu.

A cewar sanarwar, ’yan sandan sun yi nasarar kama su sakamakon wasu bayanan sirri da aka tattara da ya nuna ’yan ta’addan na shirin kai wani hari na daukar fansa ta kisan mutanensu shida da aka yi yayin ceto ba’Amurken.

Rundunar ’yan sandan ta ce tana ci gaba da aikin hadin gwiwa da takwararta ta Jamhuriyyar Nijar wajen farautar ragowar miyagun daga cikin gugun masu ta’adar da suka tsere.

Kazalika ta ce za ta gurfanar da mutanen biyu da ke hannunta a yanzu a gaban kotu da zarar ta kammala binciken da ta ke gudanarwa a kansu.