✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mutum 44 masu hada baki da ’yan bindigar Zamfara

Sojoji sun kama tirela 12 makare da shanun sata a Zamfara.

Sojoji sun kama mutum 44 masu taimaka wa ayyukan ’yan bindiga a Jihar Zamfara.

Dakarun Rundunar Operation Hadarin Daji sun kuma kama tirela 12 makare da shanun sata sama da 150 a hannun mutanen da suka shiga hannu.

“Mun gano cewa sun sayi kowace saniya ce a kan Naira 30,000 zuwa 40,000 a Kasuwar Yartasha, kafin su kama hanyar zuwa Gusau,” inji Mataimakin Kwamandan Rundunar, shiyyar Arewa maso Yamma, Air Commander Abubakar Abdulkadir.

Ya ce sojoji sun ritsa masu sayen shanun satan ne bayan dillalan sun baro Kasuwar Yartasha, a yankunan Magami da Jangeme da ke Karamar Hukumar ta Gusau.

Air Commander Abdulkadir ya ce, “Za mu ci gaba da yin bakin kokarinmu wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.”

Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Bashar Mailafiya, ya tabbatar cewa sojoji sun mika wa kwamitin kwato dabbobin da aka sace shanu 154 da rakumi daya da kuma rago daya.

Ya jinjina wa sojojin, tare da ba su tabbacin cewa kwamitin zai mika dabbobin ga masusu.

Ya ce kwamitin kan sanar a gidajen radiyo a duk lokacin da aka gano dabbobin sata domin masusu su zo su yi bayani, a ba su.