✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mutum 8 kan zargin tayar da tarzoma yayin ziyarar Buhari a Katsina

Babu wanda ya yi wa Buhari ihu yayin ziyararsa a Katsina.

‘Yan sanda sun kama wasu mutum takwas da ake zargi da tayar da tarzoma a yayin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara Jihar Katsina.

Buhari ya kai ziyarar aiki ta kwana biyu birnin na Dikko inda ya kaddamar da ayyuka da dama.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina Gambo Isah, ya bayyana cewa bayan da shugaban kasar ya kaddamar da aikin gadar kasa ta Kofar- Kaura, an samu labarin cewa wasu bata gari daga Sabuwar Unguwa sun shiga hannu kan zarginsu ta tayar da tarzoma.

Wani bincike da ‘yan sanda suka gudanar a cewar Gambo, ya nuna cewa bata gari sun yi amfani da yara ne wajen haddasa husuma a yankin ta hanyar jifan tawagar ‘yan sanda.

Ya kara da cewa wadanda aka kama suna taimaka wa ‘yan sanda a binciken da suke gudanarwa a yanzu.

A halin da ake ciki, rundunar ‘yan sandan ta karyata ikirarin cewa an yi wa shugaba Buhari ihu ‘ba ma yi’ da jifansa da duwatsu yayin ziyarar.

Jawabin Gambo na ranar Juma’a martani ne ga wani faifan bidiyo da aka yada kan cewa jama’a sun yi wa shugaban Najeriya ihu a lokacin da yake kaddamar da aikin gadar kasan Kofar-Kaura a ranar Alhamis.

Rundunar ‘yan sandan ta ce Buhari ya kaddamar da dukkan ayyukan da Gwamna Aminu Masari na jihar ya aiwatar cikin lumana da aminci.

SP Gambo ya yi kira ga jama’a da su yi watsi da hoton bidiyon da aka yada a kafafen sada zumunta.