✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mutum biyu da kokon kan mutane cikin makabarta a Kaduna

Rundunar ’yan sanda ta bayyana nasarar da ta samu na kama wasu mutum biyu da ake zargin alakarsu da kungiyar asiri tare da kokon kan…

Rundunar ’yan sanda ta bayyana nasarar da ta samu na kama wasu mutum biyu da ake zargin alakarsu da kungiyar asiri tare da kokon kan mutum a jihar Kaduna.

Kafofin watsa labarai da dama a kasar sun ruwaito Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, ASP Muhammad Jalige, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

Sanarwar ta ce da misalin karfe 11.00 na daren Juma’ar da ta gabata ce aka sanar da jami’an tsaro cewar an ga wasu mutane a wata makarbartar musulmai da ke yankin Kudenden kuma ana tsammanin wani mugun nufi ya kai su.

“Bayan samun rahoton ne jami’anmu suka bazama kuma suka yi nasarar kama mutanen biyu da suka fito daga unguwar Zaki a yankin Kabala na Jihar.

“Yayin bincike, mun gano fatanya a tare da su da kuma kokon kan mutane,” a cewarsa.

ASP Jalige ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike a kan mutanen kuma da zarar an kammala za’a gurfanar da su a gaban Kuliya.