✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama Sarakuna biyu kan harin tashar jirgin kasan Edo

An samu nasarar kubutar da mutum biyu da suka rage a hannun masu garkuwa da mutanen.

Gwamnatin Jihar Edo, ta ce ta kama sarakuna guda biyu tare da wasu mutum biyar wadanda ake zargi da hannu a garkuwa da fasinjoji 20 a harin da aka kai tashar jirgin kasa a jihar ranar 7 ga watan Janairu.

Kwamishinan Sadarwa da Wayar da Kai a jihar, Chris Nehikhare, shi ya bayyana hakan jiya Laraba a Benin, yayin zantawa da manema labarai jim kadan bayan fitowa daga taron Majalisar Zartaswa.

Ya ce jami’an tsaro sun samu nasarar kubutar da mutum biyu da suka rage a hannun masu garkuwa da mutanen.

“Mun kuma samu nasarar cafke mutane bakwai da a ake zargi ciki hara da wasu sarakunan kauye biyu.”

A ranar 7 ga watan Janairu ne, wasu da ake zargin ’yan bindiga suka kai hari tashar jirgin kasa a jihar tare da sace mutum 20.