✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama shi da kokunan kan dan Adam

An damke wani mutum mai shekara 55 dauke da kokunan kai da wasu sassan jikin dan Adam a jihar Osun. An kama mutumin da kokunan…

An damke wani mutum mai shekara 55 dauke da kokunan kai da wasu sassan jikin dan Adam a jihar Osun.

An kama mutumin da kokunan kan dan Adam hudu, hannu biyu da haba uku a unguwar a Ijebu-Igbo da ga garin Ijebu-Ode na jihar.

Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, ya ce wanda ake zargin, an kama shi a ranar Litinin bayan ya yi aika aikan a wata makabarta, ranar Litinin.

Oyeyemi ya ce an cafke mutumin ne bayan wani rahoto da aka kai wa ofishin Ago-Iwoye da ke Karamar Hukumar Ijebu ta Arewa.

Mai shigar da karar ya shaida wa ’yan sanda cewa an ga wani mutum dauke da wata jaka da ake zargin kayan sata ne a ciki, ko da aka fara tuhumarsa sai ya jefar da ita ya yi cikin daji a guje.

Sanarwar ta ce, “Bayan rahoton, DPO na Ago-Iwoye, CSP Paul Omiwole, ya jagoranci ’yan sanda zuwa wurin, suka bude jakar suka gano tana dauke ne da sassan jikin mutum”.

A yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa ya debo sassan jikin mutanen ne daga wata makabartar Kirista da ke Oke-Eri, Ijebu-Ode tare da wani wanda ya riga ya tsere.

Oyeyemi ya ce kwamishinan ’yan sanda, Edward Ajogun, ya ba da umarnin a mika lamarin nan take ga Sashen Binciken Manyan Laifuka da Tara Bayanai don kara bincike da gurfanar da wanda ke zargin.

Ya kara da cewa kwamishinan ya kuma bayar da umarnin a farauto wanda ya gudu shi ma a gurfanar da shi a gaban kotu.